Yau za a yi jana'izar Idris Deby Itno
April 23, 2021Shugabannin kasashe duniya da dama da suka hada da shugabannin Gini da Nijar da Mali da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da kuma Shugaba Emmanuel Macron na Faransa gami da kantoman da ke kula da hulda da kasashen waje na EU Josep Borrel na daga cikin wadanda za su halarci jana'izar.
Masu aiko da rahotanni sun ce an baza jami'an tsaro ta ko ina domin guje wa samun tashin-tashina yayin jana'izar, wanda a lokacin sojin kasar za su gudanar da wani biki na girmama margayin.
Rasuwar shugaban Deby ta jefa kasar da ma yankin na Sahel musamman a fanin yaki da 'yan ta'adda cikin rudani, lamarin da ya sanya jama'a tserewa zuwa kasashe makwabta domin tsira da rayukansu. Marigayin ya rasu yana da shekaru 68 wanda kuma ya shafe shekaru 30 yana mulki tun bayan jagorantar juyin mulki a shekarar 1990.