Chadi za ta bar aika sojoji a ketare
April 10, 2020Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno daga yanzu ya dakatar da aikawa da sojojin kasarsa ya ce sojojin kasarsa a cikin rundunonin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a Sahel da yankin tabkin Chadi, da ma shiga duk wasu yake-yake na waje da ba su shafi kasar kai tsaye ba.
Shugaba Deby ya sanar da wannan mataki nasa ne a wani rahoto da gidan talabijin na gwamnatin kasar ya wallafa a wannan Juma'a inda ya ce sojojin Chadi da dama sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare yankin tafkin Chadi da na Sahel, dan haka daga yanzu babu wani sojin kasar da zai sake halartar wani yaki a wasu kasashe na ketare.
A karshen watan da ya gabata ne dai dakaran sojan kasar ta Chadi a karkashin jagorancin shugaban kasar Idriss Deby suka kaddamar da wani gagarimin farmaki a tsibirran tafkin Chadi inda suka fatattaki mayakan Boko Haram daga yankin baki daya, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Chadi 52 a yayin da mayakan Boko Haram kimanin dubu suka halaka a cewar gwamnatin ta Chadi.