1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar karfafa alakar Jamus da Chaina

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2023

Firaministan Chaina Li Qiang ya bayyana cewa alaka ta kusa da Jamus da kuma kokarin cire fargaba, na da matukar muhimmanci wajen karfafa tattalin arzikin duniya da yake tangal-tangal.

https://p.dw.com/p/4SrCH
Jamus | Berlin | Olaf Scholz Ziyara | Li Qiang | Chaina
Firaministan Chaina Li QiangHoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP

Firaministan Chaina Li Qiang ya yi wadannan kalaman ne yayin ziyararsa a Jamus, kuma suna zuwa ne a daidai lokacin da Jamus din ke kokarin samun hanyar da za ta rage dogaro da Chaina. Wannan dai shi ne karo na farko da Li ya kai ziyara kasashen ketare tun bayan zamowarsa firaminista, kuma a yayin ziyarar tasa ya kara jaddada bukatar Beijing na karfafa dangantakar da ke tsakaninta da kungiyar Tarayyaar Turai EU a daidai lokacin da kasarsa ke kara fuskantar suka daga kungiyar ta EU. Li dai ya ce akwai bukatar Jamus da Chaina su hada kai wajen samar da ingantaccen muhalli, yayin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke zaman mai masaukin baki ke cewa dangantaka ta kusa a bangaren yaki da sauyin yanayi shi ne babban abin da suka fi bai wa muhimmanci a yanzu.