1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake tsaurara matakan hana yaduwar Coronavirus a Chaina

Zulaiha Abubakar MNA
May 13, 2020

Mahukunta a Wuhan yankin da annobar Coronavirus ta fara billa na shirin gudanar da wani sabon gwajin cutar tsakanin mazauna yankin da yawansu ya kusan miliyan 11 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito.

https://p.dw.com/p/3cAjG
China Wuhan | Hubei verringert die Corona-Alarmstufe
Hoto: Getty Images/AFP/Str.

Sanarwar da gwamnatin Chainar ta bayar ta kara da cewar gwamnatin kasar ba ta sanar da ranar fara gwajin ba, amma kwamitin kar ta kwana a aikin yaki da yaduwar cutar ta corona a fadin kasar ya umarci shugabannin yankuna a Wuhan su kasance cikin shiri, wannan umarni ya biyo bayan samun billar cutar a jikin wasu mutane shida.

Tun bayan da kasar ta fara farfadowa daga annobar ta COVID-19 mahukunta ke aikin dakile sake billar ta cikin gaggawa.

A wani sabon labarin kuma mahukunta a yankin Jilin da ke kan iyakar Chaina da Koriya ta Arewa sun dakatar da harkokin sufiri tare da kaddamar da sabbin dokoki biyo bayan sake billar cutar.