1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta bude gada mafi tsayi a duniya

Yusuf Bala Nayaya
October 23, 2018

Yayin da masu goyon bayan gina wannan gada ke murna da cewa dama ce ta kara samun bunkasar kasuwanci, 'yan adawa na cewa kokari ne na mamayar Hong Kong.

https://p.dw.com/p/36z5m
China Hongkong-Zhuhai-Macao-Brücke
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Kin Cheung

Shugaba Xi Jinping na Chaina a wannan rana ta Talata ya bude gada mafi tsayi da ta ratsa teku da aka taba yi a duniya. Gadar da ta hade yankunan Hong Kong da Macau da China. Aikin gina gadar da ke zuwa sa'ilin da mahukuntan birnin Beijing ke kokari na sake rike yankunansu da ke da kwarya-kwaryar cin gashin kai.

Wannan gada dai na da tsayin kilomita 55 ne. A yayin bikin bude gadar kuma da aka yi a tashar bakin ruwa ta Zhuhai shugabanni daga yankunan na Hong Kong da Macau sun halarta. Masu goyon bayan gina wannan gada na nuna murna da cewa wannan dama ce ta kara samun bunkasar kasuwanci da rage lokaci da ake batawa a tafiye-tafiye tsakanin yankunan, 'yan adawa kuwa na ci gaba da korafi na cewa kokari ne na mahukuntan birnin Beijing na sake matso da birnin na Hong Kong kusa da su bayan kwarya-kwaryar cin gashin kai da yake da shi.