1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

An daina wallafa masu kamuwa da Covid-19 a Chaina

December 25, 2022

Chaina ta bayyana kawo karshen fitar da yawan wadanda suka kamu da cutar Covid-19 da ake yi a kullum.

https://p.dw.com/p/4LQ9F
Chaina | Matsalar Covid-19
Jinyar cutar Covid-19 a ChainaHoto: HECTOR RETAMAL/AFP/Getty Images

Hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar Chaina ta ce, kasar za ta daina bayyana yawan a kullum na wadanda suka kamu ko suka mutu sakamakon annobar Covid-19. Hukumar dai ba ta bayar da wani karin bayani ba kan dokar fitar da alkalumma da ta fara aiki a shekarar 2020, kana ba ta bayyana zuwa yaushe za ta rika fitar da yawan masu dauke da cutar a kasar ba.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar za ta rika fitar da bayanai game da cutar lokaci zuwa lokaci.

A farkon wannan wata na Disamba dai hukumomin kasar suka fara sassauta dokar kullen Covid-19, biyo bayan zanga-zanga da ta barke a manyan biranen kasar. Sai dai tun bayan sassauta wasu ka'idojin yaki da annobar, mutum shida kacal Beijing ta sanar da mutuwarsu sakamakon cutar. Kazalika Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ba ta samu alkalumman masu dauke da cutar daga Chaina ba tun daga wancan lokacin.