1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta yi barazanar murkushe cin gashin kai a Taiwan

Abdullahi Tanko Bala
January 12, 2024

Kwana guda gabanin zaben shugaban kasa a Taiwan, Chaina ta ce za ta murkushe dukkan wani yunkuri na ayyana 'yancin cin gashin kai.

https://p.dw.com/p/4bBkN
Taiwan Wahlkampf 2024 | Democratic Progressive Party | Anhänger
Hoto: Carlos Garcia Rawlins/REUTERS

Sojojin Chaina  sun ce a shirye suke su murkushe duk wani yunkuri na ayyana cin gashin kai a tsibirin Taiwan a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron China.

Beijin ta zafafa barazana ga Taiwan a karkashin shugaban Tsai Ing-wen a wani mataki na karkata hankulan masu zabe zuwa ga jam'iyyun 'yan takara da ke biyayya ga Chaina.

Dubban magoya bayan jam'iyyun siyasar na Taiwan sun gudanar da taron gangami yayin da yan takara ke yakin neman zabe a rana ta karshe gabanin zaben da Chaina ta yi kashedin cewa zai iya kaiwa ga haifar da yaki a kan tsibirin. China dai na ikrarin cewa tsibirin mallakinta ne