1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Chaina za ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Gaza

October 20, 2023

Chaina ta ce a shirye take ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Isra'ila da Falasdinawa ta hanyar tattaunawa a kan teburin sulhu, la'akari da yadda yake ci gaba da lakume rayukan mutane a kullum.

https://p.dw.com/p/4Xmex
Rikicin yankin Gabas ta Tsakiya na ci wa Putin na Rasha da Xi na Chaina tuwo a kwarya
Rikicin yankin Gabas ta Tsakiya na ci wa Putin na Rasha da Xi na Chaina tuwo a kwaryaHoto: Sergei Guneyev/Pool/picture alliance

Wakilin Chaina na musamman a Gabas ta Tsakiya Zhai Jun ne ya bayyana hakan a birnin Doha na kasar Qatar, bayan ganawa da wakilin Rasha na musamman a yankin da kuma kasashen Afirka Mikhail Bogdanov, yana mai nuna takaicin kasarsa kan yadda fararen hula da ba su ji ba su gani ke asarar rayukansu a yankin Gabas ta Tsakiya. Sannan ya ce babu kuma abin da ya dace a yi face kafa kasashen Isra'ila da Falasdinu a matsayin mafita kan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa shekara da shekaru.

Karin bayani:Chaina ta jaddada goyon baya ga Rasha 

A nasa bangaren, shugaban Amurka Joe Biden na ganawa da sakatariyar zartaswa ta kungiyar tarayyar Ursula von der Leyen da kuma shugaban majalisar tarayyar Turai Charles Michel a birnin Washington, a wani taro da ake sa ran zai gabatar da jawabin neman hadin kai kan rikincin Gaza da kuma rikicin Ukraine.