Chamisa: "Ni na lashe zaben Zimbabuwe"
August 27, 2023A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Harare, Nelson Chamisa,wanda Pasto ne kuma lauya mai shekaru 45 da haihuwa, ya ce ya yi matikar mamaki da aka bayyana Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Zimbabuwe, alhali hakikanin sakamakon na nuna akasin haka.
karin bayani: Kammala babban zabe a Zimbabuwe
Hukumar zaben kasar Zimbabbuwe ta nunar da cewa Mnangagwa ya samu kashi 52.6% na kuri'un da aka kada, lamarin da ke ba shi damar gudanar da wa'adi na biyu na mulki, yayin da babban abokin hamayyarsa Nelson Chamisa ya samu kashi 44%. Sai dai masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da na (SADC) da Commonwealth suka ce wasu 'yan Zimbabuwe ba su samu damar kada kuri'a ba sakamakon rashin sunayensu a kundin zabe.
Karin bayani: Jam'iyyar CCC ta sha alwashin kayar da Zanu-PF