1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Charles III a majalisar Bundestag

March 30, 2023

Sarkin Ingila Charles III a yayin ziyarar da kai Jamus ya yi hannunka mai sanda kan girman barazanar mamayar Ukraine da Rasha ke yi ga kasashen Turai musanman ma a fannin tsaro da kuma dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/4PVQC
Charles III na jawabi a BundestagHoto: Wolfgang Kumm/dpa/picture alliance

Charles III ya yi wannan furuci ne a gaban 'yan majalisar dokokin Jamus ta na Bundestag a yau Alhamis inda ya nunar da bacin ransa kan yadda duniya ta zuba ido ta kyale Rasha tana cin karenta ba bu babbaka a Ukraine.

Sai dai ya yaba da matakin da kasarsa Ingila da kuma Jamus suka dauka na dafawa Kiev ta hanyar horon sojoji da kuma tallafin manyan makamai na zamani don ta kare kanta.

Charles III shi ne sarkin Ingila na farko da ke yin jawabi a gaban 'yan majalisar Bundestag kuma Jamus na a matsayin kasa ta farko da ya fara kaiwa ziyara tun bayan nadinsa a matsayin magajin Elizabeth II.

Ziyarar basaraken na Ingila ta kwanaki uku a Jamus wani sabon babi ne na karfafa hulda tsakanin kasashen biyu tun bayan ficewar Ingila daga cikin kungiyar tarayyar Turai a shekarar 2020.