Charles Taylor ya bayyana a kotun ƙasa da ƙasa
July 3, 2007A karo na farko, tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, ya halaraci shari´ar da kotun ƙasa da ƙasa ke yi masa, a birnin The Hage, ko kuma la Haye dake ƙasar Hollande.
Tun ranar 4 ga watan da ya gabata, a ka fara wannan shari´a, amma tsofan shugaban ƙasar ya ƙi bayyana gaban kotu.
A na zarginCharles Taylor da leffika guda 11 da su ka hada da kissan gilla, fayɗe , handama da baba kere, da dai sauran miyagun leffika masu kama da haka.
A wani taƙaitacen jawabi da yayi gaba alƙalan,Charles Taylor, ya jaddada yin wasti da dukkan lefikan da a ke zargin sa da aikatawa.
Ɗan lokaci ƙalilan bayan fara wannan shari´a, kotu ta ɗage ta, har zuwa 20 ga wata mai kamawa.
Charles Taylor, shine shugaban Afrika na farko da ya taɓa gurfana gaban kotun ƙasa da ƙasa.