1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chibok an yanka ta tashi bayan sanarwar sojin Najeriya

Zainab Mohammed AbubakrMay 20, 2016

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewar ta ceto mata da yara 97, kuma ta ce daya daga cikinsu na daga cikin 'yan matan na makarantar Chibok, sai dai uwayen yaran na Chibok sun ce yarinyar ba diyarsu ce ba.

https://p.dw.com/p/1Iqy9
Nigeria Zweites Chibok Girl befreit
Hoto: Reuters

Kakakin rundunar soji Sani Usman ya shaidar da cewar, yarinyar na daga cikin mata da yara kanana 97 da dakarun Najeriyar suka cimma cetosu da safiyar Alhamis daga 'yan kungiyar ta Boko Haram da ke garkuwa da su.

Amina Ali Darsha Nkeki, ta kasance yarin ta farko da saka ceto a kusa da garin Damboa dake kudancin garin Maiduguri dake yankin arewa maso gabashin Najeriya da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka dauki tsawon shekaru 7 suna cin karensu babu babbaka.

Jami'ai sun tabbatar da cewar Amina na daya daga cikin 'yan matan na Chibok 219 da aka sace a makarantarsu a watan Afrilun shekara ta 2014. Da yammacin jiya ne dai rundunar sojin Najeriyar ta sanar da kai somame a Damboa, wanda ya taimaka wajen ceto kusan mutane 100 da ake garkuwa dasu cikin jeji.

To sai dai a halin da ake ciki a cikin wata hira da wakilinmu na Gombe Al Amin Suleiman Mohammed ya yi da daya daga cikin iyayen na'yan matan Chibok ya shaida masa cewar babu wata yarinyar mai sunan Serah Luka da ke cikin 'yan makarantar na Chibok.