1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chibok ya sake komawa karkashin gwamnati

Pinado Abdu-WabaNovember 16, 2014

Dakarun Najeriya sun yin ikiraren amshe garin Chibok da ke yankin Arewa maso gabashin kasar daga hannun 'yan kungiyar da aka fi Sani da suna Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1DoNn
Hoto: Reuters

Dakarun Najeriya sun amshe Chibok daga hannun Boko Haram ne a karkashin jagorancin runduna ta bakwai. A wannan gari ne aka yi awon gaba da 'yan mata 'yan makaranta su sama da dari biyu fiye da watanni shidan da suka gabata.

Kakakin rundunar sojin kasar, Birgediya Janar Olajide olaleye ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Associated Press da wannan labarin, ya na mai cewa babu shakka yanzu Chibok na hannun jami'an tsaro, inda ya kuma karawa mazauna garin na Chibok karfin gwiwar komawa gida.

Idan ba a manta ba, a daren Alhamis ne garin na Chibok ya fada hannun kungiyar Boko Haram. Dubban 'yan garin ne suka tsere lokacin da ayarin 'ya'yan kungiyar ya afka wa Chibok cikin motoci kirar akori-kura da babura, inda suka hallaka da dama suka kuma kona matsugunnensu.