An fara ceto mutanen da rami ya binne a China
January 24, 2021Talla
Kafofin yada labaran kasar China sun ruwaito mahaka ma'adinan hudu da aka ceto, suna na cikin mutane 10 na farko da suka fara sadarwa da jami'an agaji bayan da ramin ya rufta da su a ranar 10 ga awatan Janairun 2021.
Rahotanni na cewa an ciro mutane hudu da rai, amma suna cikin wani yanayi na kasala da wahala. Kusan makonni biyu kenan jami'an agaji ke kokarin ceto mutane 22 da suka makale bayan da wata fashewa ta yi sanadiyar binne ramin da suke hako ma'aidinan karkashin kasa.