1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China ta zarta kasashen duniya amfani da bakin gawayi

March 30, 2021

Kasar China ke samar da fiye da rabin lantarkin da duniya ke samarwa ta hanyar bakin gawayi, lamarin da ke haifar da damuwar gurbata muhalli a tsakanin kasashe mafi karfin tattalin arziki na duniya da ake kira G20.

https://p.dw.com/p/3rMc8
Luftverschmutzung in China
Hoto: picture-alliance/AP/Imaginechina

Wani ayarin masu bincike kan lamarin da ake kira da Ember ya sanar a ranar Litinin cewa a shekarar da ta gabata China ce ta samar da kaso 53 cikin 100 na lantarkin da aka samar ta hanyar amfani da gawayi, duk kuwa da yarjejeniyar da ake da ita na cewa za ta rage amfani da gawayin don alkinta muhalli.

Masana dai na cewa amfani da bakin gawayi wurin samar da lantarkin da China ke yi shi ne mafi hadari ga muhalli a cikin hanyoyin da ake samar da lantarki a duniya.


To amma a gefe guda, masu binciken na Ember sun jinjina wa Birtaniya inda suka ce ita ce kasar G20 ta baya-bayan nan bayan Jamus da ke kauce wa amfani da bakin gawayi, ta mayar da hankali wurin amfani da iska da hasken rana don samar da lantarkin da take bukata.