1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hong Kong: Dokar tsaro mai tattare da cece-kuce

Abdoulaye Mamane Amadou
June 30, 2020

Majalisar dokokin China ta kada kuri'ar amincewa da dokar tsaro ta yankin Hong Kong mai cike da cece-kuce, a daidai lokacin da ake fargabar sake barkewar tarzoma a yankin.

https://p.dw.com/p/3eXym
Hongkong | Protest | Polizeibeamte
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Yu

Dokar na shirin kawo karshen duk wani kace-nace tsakanin masu bore da jami'an yankin hakan da ma duk wani katsalandan din kasashen ketare kan yankin mai cin kwarya-kwaryar 'yancin gashin kai daga China.

Ko da yake a yayin taronta na mako-mako shugabar yankin Carrie Lam ta ki aminta da ta fito karara ta bayyana cewa an kada kuri'ar.

Ana hasashen sake barkewar tarzoma game da sabuwar dokar wacce masu rajin girka demukuradiyya suka jima suna hankorin kawar da ita kana kuma take shan suka daga kasashen ketare ciki har da Amirka da Tarayyar Turai.