1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Sabbin kamun coronavirus sun ragu

Abdullahi Tanko Bala
February 18, 2020

Wadanda suka kamu da cutar coronavirus a lardin Hubei na China sun haura 1,886 a cewar hukumomin lafiya na kasar China

https://p.dw.com/p/3Xv7A
China Coronavirus
Hoto: Getty Images/AFP

Hukumomin lafiya a China sun ruwaito sabbin alkaluma 1,886 na sabbin kamun kwayar cutar coronavirus wanda ke zama adadi mafi karanci da aka samu a rana guda a wannan watan. Sabbin alkaluman sun kuma an sami karin mutane 98 da suka rasu a lardin Hubei.

Hukumomin na China sun ce raguwar alkaluman wata alama ce da ke nuna matakan da ake dauka na shawo kan cutar na yin tasiri.

A wannan Talatar hukumomin lafiyar a China sun ce suna aiki don samar da sabin allurai da magungunan cutar da hanyoyin tantace jinin mara lafiya da kuma kare rayuwar likitoci.

A waje guda kuma hukumomin lafiya a Japan sun ce za su fara gwajin amfani da maganin cutar HIV don warkar da marasa lafiya da suka kamu da cutar coronavirus.