China: Masu zama a Amirka su yi taka tsan-tsan
June 4, 2019Talla
Shugabannin kasar China sun koka da rashin tabbataccen tsaro da cin zarafi ga 'yan kasar idan suka je a Amirka. Wannan gargadin na kasar China ga 'yan kasarta, na zuwa ne a daidai lokacin da tsamin dangantaka da takaddama ke kara zafafa tsakanin gwamnatin Washington da Pekin kan batun cinikayya, musamman ma matakin baya-bayan nan da gwamnatin Donald Trump ta dauka kan kamfanonin China ciki har da kamfanin kera wayar salula na Huawei.