1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta soke killace matafiya don Corona

Abdullahi Tanko Bala
December 27, 2022

Matakin China na soke dokar killace matafiya da suka shiga kasar don tantance ko suna dauke da cutar Corona zai tamaka wajen farfado da harkokin yawon bude ido a fadin kasar daga maziyarta na kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/4LT79
China | Passagiere mit Masken im Flughafen Peking
Hoto: Kyodo/picture alliance

A wannan Litinin China ta sanar da cewa za ta kawo karshen dokar kullen ga matafiya daga kasashen waje.

Ana sa ran dokar za ta fara aiki daga ranar 8 ga watan Janairu.

A halin da ake ciki dai matafiya daga kasashen waje da suka shiga kasar ciki har da 'yan kasar ta China sai sun killace kansu na kwanaki biya a Otel sannan kuma su yi kwanaki uku a gida kafin su ci gaba da cudanya da jama'a.