Beijing ta yi martani ga NATO
June 30, 2022Talla
Gwamnatin China, ta yi kakkausar maratani ga kungiyar tsaro ta NATO, tare da cewa kungiyar ta tafka babban kuskure na yi mata mumunar fassara na ayyana Beijin a mastayin barazana.
Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10, da kungiyar NATO da ke taro a Spain ta ayyana Sin a matsayin karfen kafa. Zhao Lijian kakakin ma'aikatar harkokin wajen China, ya ce NATO ta bata manufufiofin Beijing.
"Nato ta yi kalamai mara dadi kan ci gaban soja da manufofin tsaron kasa na Sin, wannan da dai-dai ba ne, zai kara haddasa tashin hankali ne, kuma yana cike da tunanin yakin cacar baka da kyamar akida."