China ta yanke wa wasu 'yan Uyghur hukuncin kisa
April 7, 2021An dai yankewa jami'an Musulmai hukuncin da za a jinkirta aiwatar wa na tsawon shekaru biyu bisa laifin yunkurin ballewa da ma amsar cin hanci da rashawa.
An tuhumi Shirzat Bawudun tsohon shugaban sashin shari'a na yankin da aikata laifin baiyana asirin kasa da kuma hannu cikin wasu ayyukan ta'addanci na kungiyar ETIM.
Shi kuwa tsohon daractan illimin yankin Sattar Sawut an tuhume shi ne da sanya batutuwan da suka shafuka na tsattsaurar ra'ayin addini da rikice-rikice da kuma ballewa cikin litattafan makarantun yankin wanda kotu ta alakanta hakan da harin da aka kai babban birnin yankin Urumqi a shekarar 2009 ya kuma yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dari 2.
Gwamnatin China dai ta ce ta na ci gaba da zakulo jami'an gwamnati da ke da fuska biyu kuma suke yin zangon kasa ga mulkinta a yankin, sai dai har kawo yanzu ana zargin gwamnatin kasar da take hakkin bil adama a yankin.