1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin 'yan Kanada da leken asiri a China

Abdoulaye Mamane Amadou
June 19, 2020

Hukumomin shari'a a China sun kama wasu kwararru 'yan Kanada da aikata laifin leken asiri da yunkurin da gurbata harkokin tsaron kasar, a daidai lokacin da dangantaka ta soma tsami a huldar diflomasiyar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3e1Sc
Kanada Vancouer | Menschen fordern Freilassung von Michael Kovrig und Michael Spavor
Hoto: Reuters/L. Wasson

China ta kama wasu 'yan kasar Kanada biyu da laifin leken asiri da yunkurin kawo mata illa ga harkokin tsaro, kamar yadda wata sanarwar daga ofishin babban alkalin kasar ta bayyana a yau Juma'a.

Hukumomin kasar dai sun cafke Michael Kovrig wani tsohon jami'in diflomasiya tare da Michael Spavor kwararre kan harkokin kasa da kasa musamman da suka shafi Koriya ta Arewa ne a cikin watan Disamban shekarar 2018, lamarin da ya haifar da wani yanayi na gurbacewar dangantaka tsakankanin kasashen biyu na Kanada da kasar ta China.