Masana sun gano yiwuwar annobar murar Aladu
June 30, 2020Talla
Masu binciken kimiyya a China sun gano wani sabon nau'in cutar murar Aladu da za ta iya zama annoba a duniya kamar yadda binciken da aka wallafa a ranar Litinin da ta gabata a mujallar kimiyya ta Amirka ya nunar.
Sai dai wasu masana na cewa a yanzu cutar bata da wani hadari na gaggawa.
Kwayar cutar na yaduwa a tsakanin mutane kuma akwai bukatar sa ido sosai ko da za ta zama annoba a cewar wadanda suka wallafa binciken da suka hada da masana kimiyya daga jami'oin China da kuma cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta China.
Daga cikin kwayoyin cuttukan da masanan suka gano sun hada da nau'in G4 na kwayar cutar H1N1 wadda ke da dukkanin alamu na iya zama annoba.