1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya da Turkiyya: Ci gaba da aikin ceto

Mahamud Yaya Azare LMJ
February 15, 2023

Kwanaki tara bayan girgizar kasar da ta afka a Turkiyya da Siriya har yanzu ana ci gaba da zakulo mutane da ransu, bayan afkuwar ibtila'in da a yanzu haka ya lakume rayukan fiye da mutane dubu 41.

https://p.dw.com/p/4NXLw
Girgizar Kasa | Siriya | Turkiyya | Aikin Ceto
Masu aikin ceto na ci gaba da kokari a Turkiyya da SiriyaHoto: Tunahan Turhan/ZUMA/IMAGO

Masu aikin ceto sun yi nasarar zakulo wata tsohuwa 'yar shekaru 77 mai suna Fatima da ta shafe kwanaki tara makale a karkashin barakuzan gine-ginen da girgizar kasa ta rusa a birnin Adiyaman na kasar Turkiya, a ci gaba da aikin laluben wadanda suka makale a karkashin gine-gine da jami'an agaji ke yi. Masu aikin agaji daga chaina da suka yi nasarar zakulo tsohowar sun ce, abun ya matukar ba su mamaki. Cikin wadanda akai mamakin zakulowa da ran nasu har da wata jaririya da aka haifa cikin barakuzan kuma mahaifiyarta ta rasu, inda aka sanya mata suna Ayah wato Ayar Allah. A yanzu haka dubun-dubatar mutane daga ko ina a duniya na rububin neman a ba su ita domin su rainonta, cikinsu har da ma'aikacin agajin da ya zakulota. An kuma samu wata yarinyar da jim kadan bayan zakulo mahaifiyarta daga cikin burakuzai aka haifeta, wacca shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan da kansa ya rada mata suna Aisha Batulu wato budurwa mai tsawan rai kana ya yi mata kiran sallar radin suna.

Siriya | Girgizar Kasa | Jaririya | Aikin Ceto
Jaririya Aya da aka haifa a cikin barakuzan girgizar kasaHoto: Ghaith Alsayed/AP/picture alliance

Ci gaba da zakulo masu rai da gawarwakin da ake ta yi a bangaren kasar Turkiya ba ya rasa nasaba da aikin da dubban ma'aikatan agaji ke yi, inda tauraron dan Adam kimanin 257 ke bai wa ma'aikatan taswirorin wuraren da mutane ke makale. Sai dai abin ba haka yake ba a bangaren kasar Siriya, inda ayarin farko na motocin agajin Majalisar Dinkin Duniya suka shiga yankin 'yan tawayen na Siriya mako guda bayan girgizar kasar. Sai da shugaban Siriya Bashar al-Assad ya amince ne aka fara shiga Siriyan lamarin da ke ci gaba da janyo cece-kuce kan neman izininsa da Majalisar Dinkin Duniya ta yi da cewa hakan na ba shi halaccin shugabantar kasar. A yanzu haka dai alkaluman wadanda suka rasu a kasashen na Turkiyya da Siriya sun zarta dubu 41, a yayin da ake fuskantar matsalar karancin magungunan ceton rayukan dubun-dubatar mutanen da ke yankin Siriya da dama can suke kukan targade sai kuma ga karaya.