Binciken kisan dan jaridar Saudiyya a Istanbul
October 17, 2018Makonni biyu bayan batan dabon shahararren dan jaridar nan na kasar Saudiyya Jamal Ahmad Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar mahukuntan kasar, sannu a hankali bayanan da ke fitowa daga bangarori daban-daban na kara tabbatar da zargin da ake yi wa mahukuntan na Riyadh da hallaka dan jaridar a cikin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na Turkiyya. Sai dai har kawo yanzu in ba ya ga dan hurjin mage irin na cikon sunna da manyan kasashen duniya irinsu su Amirka da ma kasashen Turai suka yi na nuna bacin ransu game da wannan lamari, babu wani mataki da suka dauka na matsawa Saudiyyan lamba, kamar yadda suka saba yi wa wasu kasashe a duk lokacin da aka ce sun aikata wani laifi na take hakkin dan Adam.
To amma da yake tsokaci kan wannan batun Francois Dupaire wani mai sharhi kan al'amura da suka shafi kasar Amirka ya ce dangantar sako-sakon da kasar ta Amirka ke yi kan wannan batu, na da alaka da girman huldar cinikayyar da ke akwai tsakanin kasashen biyu. Kasashen Turai wadanda suma ga al'ada ke saurin daukar mataki kan wata kasa da ke take hakkin dan Adam a wannan karon sun yi sako-sako kan wannan batu, yayin da kasashen Turan kamar Jamus yanzu haka ke ci gaba da sayar wa Saudiyyan da makamai. Koma dai me ake ciki yanzu duniya ta kasa kunne domin jin yadda sakamakon binciken kisan dan jaridar zai kasance, da kuma yadda za ta kaya tsakanin kasar ta Saudiyya da manyan kasashen duniyan.