1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da gumurzu a Aleppo na Siriya

Usman Shehu Usman
October 2, 2016

Ana can ana barin wuta tsakanin sojan gwamnati da 'yan tawayen Siriya don kwace iko da birnin Aleppo

https://p.dw.com/p/2Qooz
Syrien Kämpfe um Aleppo
Hoto: picture-alliance/AA/Abaca/M. Al Halebi

Hakan na faruwa ne bayan da aka ruwaito cewa sojojin gwamnati na kara kutsa kai cikin yankunan da ke hannun 'yan tawayen, inda suka kwace unguwanni da tsaunuka da dama daga hannu 'yan tawayen. A tsawon yinin 'yau Lahadi an ci gaba da kai wa juna farmaki, inda a hannu guda sojojin gwamnati suka tunkari gabashin birnin da ke zaman babban tungar 'yan tawaye a tsahon lokacin da suka kwashe suna wannan yakin basasa da aka kwashe sama da shekaru biyar ana gwabzawa. A bangaren sojojin gwamnatin Siriyan sun fitar da wata sanarwa tare da yin kira ga 'yan tawaye da su ajiye makamai, kana a basu damar ficewa salun-alun daga birnin. An dai bada rahotanni cewa fararen hula na cikin halin tasku, wadanda yanzu haka ke tsakiyar fagagen daga ta ko wanne bangare.