Ci gaba da muhawara a Jamus game da tura makamai Iraki
August 25, 2014Talla
Har yanzu ana ci gaba da tabka muhawara a Jamus game da aniyar gwamnatin kasar na ba wa mayakan Kurdawa na Peshmerga makamai don su yaki masu kaifi kishin addini na kungiyar IS, masu da'awar kafa daular Islama. A wata hira da tashar telebijin ta ZDF, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Jamus za taimaka da makamai amma ba za ta tura sojojinta Iraki ba.
Sannan sai ta kara da cewa: "muna da zabi guda biyu. Ko dai mu tura makamai a matsayin gudunmawarmu don kawo karshen ayyukan ta'addanci tare da hana aukuwar wani kisan kare dangi, ko kuma mu ce a'a kasadar ta yi mana girma. Sai dai mun ga cewa yanzu kam akwai dalilai na daukar mataki."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe