1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Kokarin komawa teburin tattaunawa

Lateefa Mustapha Ja'afar LMJ
December 23, 2021

Bangarorin da ke tattauna batun yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma tsakanin Tehran din da kasashe shida masu fada a ji a duniya a shekara ta 2015, za su koma kan teburin tattaunawa.

https://p.dw.com/p/44ld8
Österreich | Atomgespräche mit dem Iran
Har yanzu an gaza cimma matsaya, kan komawa yarjejeniyar nukiliyar ta 2015Hoto: EU Delegation in Vienna/Handout/AFP

Ma'aikatar hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai EU, ta ce wakilan kasashen Chaina da Faransa da Jamus da Rasha da Birtaniya da kuma Iran din ne za su halarci tattaunawa. Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta nunar da cewa tattaunawar tasu za ta mayar da hankali wajen ganin yadda Amirka za ta koma cikin yarjejeniyar da ake wa lakabi da JCPOA, bayan fitar da ita da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi da kuma yadda za a cimma matsaya mai inganci a tsakanin bangarorin biyu.