Ci gaba da tsare Mubarak na Masar
May 13, 2011Ma'aikatar shari'a ta ƙasar Masar ta ƙara kwanaki sha biyar akan wa'adin da ta ɗiba na tsare tsohon Shugaban ƙasa Hosni Mubarak da juyin juya hali yayi awan gaba da kujerarsa ta mulki. A cewar Kamfanin dillancin labarai mallakar gwamnatin ƙasar, dalilin tsawaita kwanakin tsare hambararren shugaban, na da nasaba da zargi cin hanci da karbar rashawa da ake masa.
Shugaba MUbarack mai shekaru tamanin da uku da haihuwa, da kuma mai ɗakinsa na tsare a wani asibiti da ke wurin shaƙatawa na Sharm el-Scheikh. Masu gabatar da ƙara dai sun yi masa tambayoyi iri daban-daban na tsawon sa'o'i uku a jiya alhamis, musamman ma dai game da amfani da ƙarfin tuwo da gwamnatinsa ta yi wajen murƙushe masu zanga-zangar neman sauyi a 'yan watannin da su ka gabata.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu