1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zaman makoki bayan rasuwar Sarki

June 6, 2014

An binne mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu sakamakon doguwar rashin lafiya bayan da ya shafe shekaru 51 a kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/1CDfI
Hoto: Thomas Mösch

Dubban mutane daga bangarorin daban-daban na Najeriya suka halarci sallar gawar da suka hada da mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo da sauran sarakunan gargajiya da masu karfin fada aji.

Tun farko da safiwar Jumma'a (06.06.2014) masarautar Kano da kuma gwamnatin wannan jiha suka bayyana cewa Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rasuwa, sakamakon doguwar rashin lafiya da ya yi fama da ita. Marigayin na daga cikin sarakunan Kano da suka yi dogon zamani inda ya shafe shekaru 51 a kan karagar mulki.

Sarkin Kano Ado Bayero wanda ya hau kan kujerar mulki tun a shekarar 1963, ya rasu ne bayan da ya shafe shekaru 84 a duniya. Mai martaba Alhaji Ado Bayero tsohon ma'aikacin banki ne kuma ya yi aikin dan sanda, baya ga taba zama dan majalisar dokoki da kuma jami'in diplomasiya.

Tuni dai shugaban Najeriya Goodluck Jonathan cikin wata sanarwa ya bayyana rasuwar Sarkin Kano a matsayin babban rashi ga Najeriya baki daya. Jonathan ya ce za a tuna da Alhaji Ado Bayero a matsayin mai son zaman, wanda kuma ya kulla dankon zumunci da al'ummomin daban-daban na kasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman