1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban ɓarin wuta tsaknain sojojin gwamnati da yan takife a Pakistan

October 9, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8s

Kimanin dakaru 130, masu tsatsauran kishin addinin Islama, da sojoji 45 na gwamnatin Pakistna su ka rasa rayuka, a wata bata kashi da aka gwabza tsaknain ɓangarorin 2 , kusa da iyakokin Afghanistan da Pakistan.

Cemma irin wannan mummunan artabu ya wakana ranar lahadi da ta wuce, a yankin Waziristan.

A cewar kakakin gwamnatimn Pakistan, rikicin ya ɓarke bayan da wata ƙungiyar yan takife, da abkawa sojojin gwamnati, a yayin da su ke sintirin da su ka saba lokaci zuwa lokaci, domin tabbatar da tsaro.

Bayan sojojin da su ka rasa rayuka, akwai ƙarin wasu 12 da ba a gano ba har ya zuwa yanzu.

DakarunTaliban da na Alqa´ida, sun alƙawarta gama ƙarfi, domin yaƙar shugaba Pervez Masharaf da su ke ɗauka tamkar ɗan amshin shatan Amurika.

A nata gefen,ƙasar Amurika na ɗaukar yankin Waziristan, a matsayin sansanin ƙungiyoyin ta´ada, a game da haka ta ke matsa ƙaimi ga hukumomin Islamabad, su matsa lamba wajen tsarkake wannan yanki.