Ci-gaban-zanga zanga a Togo
August 22, 2012Haɗin gwiwar ƙungiyoyin fara hula da na yan siyasa da ake kira da sunnan Sauvons le Togo ko kuma mu ceci Togo wanɗanda suka ƙunshin ƙungiyoyin fara hula guɗa tara da jam'iyyun siyasa.Su ne suka shirya wanan zanga zanga domin tilasa wa hukumomin da su soke wata ayar doka da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuria'ar amince wa da ita ba tare da yardda sauran jam'iyyun siyasar ba.
Yan adawar dai na buƙatar da a jinkirta zaɓen domin samun damar yin gyaran fuskan akan dokokin zaɓen, kafin zaɓen yan majalisun da za a gudanar a cikin watan Oktoba mai zuwa to sai dai gwamnatin ta yi watsi da buƙatar su. Tun da farko hukumomin sun haramta gangamin siyasar da yan adawar suka tsara gudanar a kwanaki ukku jere tun daga ranar Litini har ya zuwa Larba.
An sha arangama tsakanin yan sanda da masu zanga zangar
An dai sha arangama tsakanin masu yin yamutsin da yan sanda a wurare da dama inda jami'an tsaron suka ja daga kafin daga bisanni jama'ar da suka gaɓce su ci ƙarfin su da jifa da duwarwatsu;Abinda ya sa jami'an tsaro suka ja da baya domin ƙara yin shirin.Masu gudanar da yamutsin da suka fuskanci yan sandar suka riƙa harba masu barkonon tshohuwa da harsashen roba abinda ya kaste hamzarin marcin da aka so yi har ya zuwa tsakiyar birnin Lome a dandalin yanci na Deckon,amma bai hanna su raira waƙen sukar lamirin gwamnatin ba.
Yan adawar na buƙatar da a jinkirta zaɓen
Matasa sun ƙone tayoyi tare da saka shingaye akan tituna abinda ya kawo cikas akan sha'anin zirga zirga a tsakiyar birnin inda hada hada ta kasuwanci ta tsaya cik Hukumomin sun ba da sanarwa cewar jama'a da dama ne suka jikata yayin da kuma wasu ake tsare da su a ofishin yan sanda.Yan adawar na cewar dokar da aka ɓulo da ita a cikin kundin zaɓen ta fi gyara jam'iyyun siyasar da ke yin mulki; sannan da ƙarin da aka samu na yan majalisun dokoki daga 81 zuwa 91.
Shugaba Faure Gnassingbe ya zo ne kan ragamar mulkin bayan mutuwar mahaifin sa a wani zaɓen da aka shirya a shekara ta 2005 wanda ke cike da kura kurai na maguɗi kafin a shekara ta 2010 a sake zaɓen sa a matsayin shugaban ƙasa wanda shi ma yan adawar ƙasar suka ce ya yi murɗiya a ciki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto