1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

050712 Algerien Unabhängigkeit

July 5, 2012

Al'ummar Aljeriya sun koka game da mawuyacin rayuwar da suke ciki shekaru 50 bayan samun 'yanci.

https://p.dw.com/p/15S5e
Algerian actors reenact the Algerian war against France during the celebration of the 50th anniversary of their independence from France, which occupied Algeria for 132 years, in Algiers July 5, 2012. REUTERS/Louafi Larbi (ALGERIA - Tags: ANNIVERSARY ENTERTAINMENT SOCIETY)
Bukukuwan cika shekaru 50 da 'yanciHoto: Reuters

A wannan Alhamis ce al'ummar Aljeriya suka gudanar da shagulgulan cika shekaru 50 da samun 'yancin ƙasar, a dai dai lokacin da 'yan ƙasar da dama ke nuna ta'ba'ba game da makomar ƙasar, kana wasun su ma ke hasashen yiwuwar ɓarkewar boren adawa da gwamnati kwatankwacin na ƙasashen Larabawa saboda rashin kyakkyawan shugabanci.

A dai ranar 5 ga watan Yulin shekara ta 1962 ne ƙasar Aljeriya ta samu 'yancin ta daga Turawan mulkin mallakar Faransa, wanda a matsayin wani ɓangare na bukukuwan ne gwamnati ta ɓullo da sabuwar ƙwandalar cikar ƙasar shekaru 50. Sa dai kuma ba kowane ɗan ƙasar ne ke jin daɗin shagulgulan ba saboda manufofin da gwamnatin ƙasar ke aiwatarwa ba sa kyautata rayuwar su. Wanna kuwa na faruwa ne duk da cewar ƙasar tana da ɗimbin arziƙin man feture da iskar gas, da ke samar mata da ɗimbin kuɗaɗen shiga amma ba tare da 'yan ƙasar sun gani a ƙasa ba.

Martanin 'yan ƙasar game zagayowar ranar samun 'yanci

Abdelaziz Bouteflika ARCHIV - Der algerische Präsident Abdelaziz Bouteflika (Archivfoto vom 08.07.2005) hat den ölreichen Staat ein Stück weit beruhigt und fitter fürs 21. Jahrhundert gemacht. Am kommenden Freitag (02.03.2007) wird der erfahrene Staatspräsident 70 Jahre alt. Foto: Stephen Pond (zu dpa-Korr. "Autoritärer Aussöhner nach blutiger Zeit: Algeriens Bouteflika 70" vom 23.02.2007) ACHTUNG: Nur zu redaktioneller Verwendung +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaba Abdelaziz BouteflikaHoto: picture-alliance/dpa

Wannan wasu yara ne ke wasannin ƙwallon ƙafa akan titunan birnin Kasbah mai daɗaɗɗen tarihi a ƙasar ta Aljeriya, inda kuma wasu 'yan ƙasar irin su Kamel Ousmane ke ganin cewar akwai wasu muhimman abubuwan tarihin da zai yi wuya ƙananan yaran su lura da su, idan aka waiwayi tarihin ƙasar shekaru 50 bayan samun 'yanci. Akan hakane ma Kamel Ousmane matashi ɗan shekaru 30 a duniya, wanda kuma ya ƙware a fannin tattalin arziƙi saboda karatun da yayi a ƙasar Faransa ya ke taƙaicin inda matsalar take:

" Ya ce abinda ba sa ganewa har yanzu shi ne magana ce ta sha'anin tafiyar da tattalin arziƙi da batun shari'ah. Ba dai dai bane mutane suna sata suna handamar dukiya kuma ba'a yi musu komi. Matuƙar hakan ya ci gaba kuma ba'a samar da gyara a ɓangaren shari'ah ba, to, abubuwa za su ci gaba da lalacewa."

Kamel Ousmane ya yi amannar cewar lokaci ya yi daya kamata tsoffin jini a harkokin mulkin Aljeriya su ja gefe su baiwa matasa damar shiga cikin sha'anin jagoranci, kasancewar a yanzun na da ake batu rubu'in 'yan Aljeriya 'yan ƙasa da shekaru 15 ne, a yayin da mafi rinjayen 'yan ƙasar kuwa shekarunsu basu zarta 30 a duniya ba.

Akwai da dama daga cikin matasan da ba su da aikin yi kuma suke gararamba akan tituna, wasunsu ma har takardun shaidar zama 'yan ƙasar ta Aljeriya ne suka ƙona saboda matsananciyar rayuwar da suke ci, yayin da wasu kuma ke ta neman hanyar zuwa Turai domin samun rayuwa mai inganci, maimakon yin anfani da su wajen gina ƙasa:

" Ya ce ana buƙatar waɗannan matasa su taka muhimmiyar rawa cikin harkokin ci gaban ƙasa. Su ƙirƙiro da abubuwa kamar kanfanoni. Idan suka yi hakan to, za su kyautata rayuwar su kuma hakan na matsayin ci gaban ƙasa ne."

epa02578185 Algerian protesters chant slogans during a demonstration on 12 February 2011 in Algiers,Algeria. The protesters demand the departure of Algerian President Abdelaziz Bouteflika . EPA/MOHAMED MESSARA +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture alliance/dpa

Mafita domin kaucewa tashin hankali irin na ƙasashen larabawa

A lokacin guguwar neman sauyin da ta kaɗa a ƙasashen Larabawa, hukumomin Aljeriya na ta yin dukkan mai yiwuwa domin tabbatar da cewar babu wani boren daya ɓulla a ƙasar, amma kuma a cewar AbdurRahim, wani magidanci a birnin Kasbah fushin 'yan ƙasar game da rashin ingancin rayuwa sai ƙaruwa take yi:

"Yace muna buƙatar matsugunai da aikin yi kana da ingantacciyar rayuwa. Muddin 'yan siyasa ba su ɗauki matakan gyara lamura ba, to, kuwa ba za'a ɗauki tsawon lokaci ba Aljeriya ma guguwar neman sauyin za ta rutsa da ita."

Lokaci ne kawai zai nuna halin da Aljeriya za ta kasance yayin da tsoffin jini ke ci gaba da riƙe madafun iko, kana matasa ke kokawa game da rashin ingancin rayuwa - shekaru 50 bayan samun 'yanci.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman