Cikas a yaki da Ebola
October 6, 2014Rashin kayan aiki da ruwan sama mai karfi sun kawo cikas a ayyukan da dakarun Amirka suke yi na taimakawa wajen yakar cutar Ebola a yankin yammacin Afirka. Sai dai a yanzu sojojin sun ce sun shirya tsaf wajen samar da tantuna da kuma asibitocin wucin gadi a Laberiya domin yakar wannan cuta.
Daya daga cikin sojojin Amirkan Laftanar Kanar Jason Brown ne ya shaida wa manema labarai hakan a Monrovia babban birnin kasar ta Laberiya, inda ya ce suna sa ran fara aikin samar da asibitocin da za su kula da ma'aikatan lafiyar da suka kamu da cutar Ebola a Litinin din nan. Cutar dai ta fi daukar rayuka a Laberiya, kasar da har kawo yanzu take fuskantar karancin gadajen kwantar da masu wannan cuta da kuma kayan aiki.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo