Cin hancin da rashawa a kamfanin man Najeriya
June 27, 2012A yayinda ake jan daga a game da hukunta mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa a harkar man fetir din Najeriya, gwamnatin ƙasar ta yi garambawul a kamfanin kula da albarkatun man ƙasar NNPC inda aka kori babban Daraktan kamfanin a abinda ke nuna daukan sabon salo ga yadda ake gudanar da harkokin kamfanin na NNPC da ma matsin lamba na hukunta wandan ake zargi da cin hanci a harakar man ƙasar.
Matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na sallamar babban daraktan kamfanin kula da albarakatun man fetir ɗin Najeriya da ma wasu manyan daraktocin kamfanin tare da naɗa Dr. Andrew Yakubu a matsayin sabon babban daraktan NNPC ɗin bai kasance da bazata ba, sanin irin ja in ja da aka daɗe ana yi a game da yadda shugabanin suke gudanar da harkokin man Najeriyar, da bincike ya nuna sama da faɗi da aka yi a yadda aka gudanar da batun kuɗaɗen tallafin man fetir.
Koda yake shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya bayyana wannan mataki da ya ɗauka a matsayin ci gaba da aiwatar da manufofi na ci gaba, to sai dai ga irin kalaman da yayi amfani da su na nuna godiya ga tsoffin shugabanin da ke tsakiyar zargin yin ba dai dai ba a harakar man Najeriyar ya sanya Comrade Abbayo Nuhu Toro na ƙungiyar ƙwadagon Najeriya da suka kasance kan gaba a kan matsawa gwamnati ya bayyana da cewa lamari ne da basu lamunta ba.
Buƙatar hukunta dukkan masu hannu a baɗakalar
Sanin cewar an gudanar da wannan sauyi ne a dai dai lokacin da gwamnatin ke ci gaba da fuskantar matsatin lamba na lallai sai ta hukunta ɗaukacin mutanen da ake zargi da yin sama da fadi da kudadden tallafin man fetir a ƙasar, duk kuwa da kace nace da lamarin ke haifawar. Irin wannan mataki na sallamar shugabanin da ake zargin suna da hannu dumu dumu a batun cin hanci da rashawa a Najeriya da a mafi yawan lokuta a kan mance da batun ya sanya tambayar shin mecece mafita? Abinda injiniya Haruna Mohammed ya bayyana da cewa mafita dai guda ce:
A yayin da gwamnatin ke ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan wannan harkar, abin jira a gani shine ko gwamnati zata iya hukunta wadanda ake zargi a dai dai lokacin da take ci gaba da gudanar da sauye-sauye a fanin man fetir ɗin ƙasar.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal