Cinikin kuri'u na neman gagarar kundila
December 19, 2022Kama daga ita kanta Hukumar Zaben Tarrayar Najeriyar ta INEC ya zuwa ga masu takama da siysar kasar da ma masu neman samo ta a daidai, hankali na dada tashi bisa sabuwar al'adar cinikin kuri'ar da ke ta yaduwa cikin kasar. Ya zuwa yanzun dai jami'an tsaron Najeriyar sun yi nasarar cafke da dama a sassan kasar a cikin sabuwar sana'ar da ke dada tada hankali ta 'yan Najeriya.
Duk da cewa cinikin kuri'ar na zama tsohuwar al'ada, amma sake tayar da ita a cikin sabon sauyi da sabon zaben zaben ke shirin ya gudana a kai na dada jawo na damuwa bisa manufa ta masu siyasa ta kasar. Zainab Minu da ke zaman kakaki a hukumar zaben ta ce bata lokaci ne cikin kasar da masu siyasar ke yia kokari na neman cika buri.
Dokar zabe ta Najeriya ta tanadi dauri da tara mai tsanani bisa dillallan kuri'ar da ke kara nuna alamun mutuwa ko yin rai cikin fage na siyasa ta kasar. Daga dukkan alamu, al'adar na jawo rike baki ga masu tunanin a karon farko anan shirin ganin daban a fagen siyasa ta Najeriya, a cewar Yunusa Tanko, jigo a jam'iyyar Labor Party.
Duk da cewar har ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki hankali na dabarar saye kuri'ar, amma daga dukkan alamu ana shirin ganin daban a kwanakin dake tafe cikin neman cin zaben a bangare na masu siyasar da mafi yawansu ke gwadawar karshe na neman mulki.