1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin makamai ya bunkasa a duniya- SIPRI

Abdul-raheem Hassan M. Ahiwa
December 5, 2022

Cinikin makaman da kamfanonin duniya ke yi ya karu, duk da cewa matsala dangane da tsarin rarraba makaman ya haifar da gagarumar koma baya a duniyar.

https://p.dw.com/p/4KUIp
Bindigogi kirar AK 47
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Zinken

Cinikin makamai da sauran kayan yaki irin na sojoji ya karu a bara. A cewar sabon rahoton masu bincike na cibiyar nazarin zaman lafiya a duniya wato SIPRI. Bukatar makaman ta karu a duniya amma harkar kasuwancinsu ta fuskanci tsaiko sakamakon annobar corona da kuma yakin Ukraine.

Manyan kamfanonin sarrafa makamai 100 na duniya, sun sayar da makamai da suka kai dala biliyan 592 a shekarar 2021, kwatankwacin kashi 1.9 cikin 100 fiye da na shekarar da ta gabata, in ji sabon rahoton SIPRI. Duk da haka ci gaban ya yi tasiri sosai saboda jan kafa da aka samu na kai makaman inda suka dace.

Yanzu haka dai kamfanonin Amirka ne ke kan gaba wajen mamaye kasuwar sarrafa makamai a duniya, wanda ke samar da fiye da dala biliyan 299 na cinikin makaman da ake yi a duniyar.

Sojan gwamnatin Angola tare da makaminsa
Sojan gwamnatin Angola tare da makaminsa Hoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Haka ma cinikin makamai daga manyan kamfanoni takwas na kasar Sin wato China, ya karu da kaso 6.3% inda ya kai dala biliyan 109 a shekarar da ta gabatan. Su kuma kamfanonin kasashen Turai suna a matsayi na 27 ne cikin manyan kamfanonin masu kera makamai 100 a duniyar. Suna kuma samun cinikin dala biliyan 123, sama da kashi 4.2 idan aka kwatanta da shekarar 2020.

Rahoton ya kuma yi nuni da yadda kamfanoni masu zaman kansu ke sayen kamfanonin makamai, lamarin da marubuta rahoton SIPRI ke cewa ya kara fitowa fili a cikin shekaru uku ko hudu da suka wuce. Wannan yanayin na barazanar sanya masana'antar kera makamai yin buya, saboda haka da wuya a iya gano su.

Kamfanoni masu zaman kansu za su sayi wadannan kamfanoni sannan kuma a zahiri ba za su samar da wani bayanan kudaden da ake samu bisa tsari ba.