1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Clinton na ziyara a Aljeriya game da rikicin Mali

October 29, 2012

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta isa kasar Aljeriya don ganawa da mahukuntan kasar dangane da shirin da ake na daukar matakin soji kan 'yan tawayen Mali

https://p.dw.com/p/16Yrw
U.S. Secretary of State Hillary Rodham Clinton delivers remarks during a press conference at the U.S. Consulate in Vladivostok, Russia Sunday, Sept. 9, 2012. (AP Photo/Jim Watson, Pool)
APEC Hillary Rodham Clinton Russland WladiwostokHoto: dapd

Da ya ke zantawa da manema labarai game da tattaunawar da Uwargida Clinton za ta yi da shugaba Abdelaziz Bouteflika da muƙarraban gwamnatinsa, ɗaya daga cikin jami'an jakadancin Amurka da ke wa Clinton din rakiya, ya ce za su gana ne da mahukuntan Aljeriyar ne kasancewar ta na daga cikin ƙasashen da ke da ƙarfin faɗa a ji a yankin Sahel kuma ake kyautata zaton za ta iya agazawa wajen kawo ƙarshen rikicin ƙasar.

Ziyarar ta sakatariyar harkokin wajen ta Amurka dai na zuwa ne bayan da a farkon wannan watan da mu ke ciki kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da wani ƙuduri da zai share fage ga kungiyar ECOWAS ko CEDEAO na yin amfani da karfin soji wajen karɓe iko da arewacin na Mali, matakin da masu sanya idanu kan rikicin Mali ɗin na cigaba da yin muhawara dangane da sahihancin ko akasain haka.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal