1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP23: An kammala taron duniya kan sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
November 17, 2017

Shugabannin duniya a taron muhalli sun jaddada karin ci gaba da matakan kare sauyin yanayi, sai dai kasashe masu tasowa sun ce har yanzu su na jira a cika musu alkawarin tallafi.

https://p.dw.com/p/2nqVY
UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Espinosa & Macron Bainimarama & Merkel & Guterres
Hoto: Reuters/W. Rattay

An kammala taron majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi da ya gudana a birnin Bonn domin tsara jadawalin aiwatar da yarjejeniyar Paris ba tare da cimma wata madafa ba, duk da cewa matakin Amirka na janyewa daga yarjejeniyar ta Paris bai sanyaya gwiwar kasashen duniya na ci gaba da yarjejeniyar ba.

Sai dai kuma duk da adawar da Trump ya nuna ga yarjejeniyar wasu wakilan Amirkar sun halarci taron inda suka fuskanci kalubale daga kasashe kimanin 200 a muhawarar ta kare sauyin yanayi.

UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Emmanuel Macron, Präsident Frankreich
Hoto: Getty Images/AFP/L. Schulze

Kungiyar kare muhalli ta Greenpeace ta ce Amirka ta gaza wajen hana  kasashen duniya ci gaba da tattaunawa domin ciyar da batun kare muhallin gaba.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasashen Turai za su yi karo-karo domin cike gibin da za a samu na kudi a sakamakon janyewar Amirka .

Wani jami’in kungiyar tarayyar Turai yace bai taba ganin taron muhalli mai raunin karsashi kamar wannan na COP23 ba, yana mai cewa duniya na bukatar daukar matakan gaggawa domin aiwatar da yarjejeniyar Paris don kare muhalli.

Deutschland Bonn - Weltklimakonferenz COP23
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Berg/

A shekarar 2015 ne dai kasashen duniya suka cimma yarjejeniyar rage dumamar duniya da kasa da maki biyu a ma’aunin Celcius.

Kasashen masu tasowa karkashin inuwar kungiyar G77 da kuma China sun ce an yi nasara a matakai da dama na tattaunawar da sai dai kuma su na bukatar ganin an cika alkawarin taimakawa kasashe masu rauni domin shawo kan matsalar sauyin yanayin.