1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin kasashen Turai na karfafa matakan yakar corona

Ramatu Garba Baba
October 29, 2020

Faransa ta aiyana dokar kulle a karo na biyu a sakamakon yadda cutar corona ke ci gaba da yaduwa ba kakkautawa, hakazalika Jamus ta dauki matakin rufe gidajen abinci da wuraren kallo.

https://p.dw.com/p/3ka4y
Italien Corona-Pandemie | Fast 98.000 Corona-Todesfälle in Europa
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Furlan

Faransa ta aiyana dokar kulle a karo na biyu tun bayan bullar annobar corona, a kokarinta na shawo kan cutar  da ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a kasar. Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da daukar matakin a daren jiya Laraba a jawabin da ya gabatar ma 'yan kasa ta kafar talabijin. 

Yaduwar cutar, batu ne da ya zo mana da mamaki inji Shugaba Macron a yayin gabatar da jawabinsa. A Jamus kuwa, mahukunta sun amince da a rufe duk gidajen sayar da abinci da gidajen kallo a dokar da za ta soma aiki daga ranar biyu ga watan Nuwamba mai zuwa.

A kasar Indiya kuwa, mutum fiye da miliyan takwas cutar ta kama kamar yadda alkaluma suka nunar a wannan Alhamis, baki daya cutar ta kama mutum sama da miliyan arba'in da hudu, mutum miliyan daya da dari biyu ta hallaka tun bayan bullarta a Disambar bara. A dai wani lokaci a wannan Alhamis, shugabanin kasashen Turai za su gana ta bidiyo don duba sabbin matakan daikile annobar da kawo yanzu ta salwantar da rayuka tare da gurgunta tattalin arzikin duniya.