1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: IAEA za ta bawa kasashen tallafi

Ahmed Salisu
April 2, 2020

Hukumar IAEA ta Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu kan makamashin nukiliya ta ce za ta aike da kayan gwajin cutar nan ta Coronavirus zuwa ga kasashen kimanin 40 a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/3aL4H
Coronavirus Hannover Testproben im Tiermedizinischen Labor
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Steffen

A wata sanarwa da ta fidda a jiya Laraba, hukumar ta ce ta dau wannan matakin ne domin ganin an samu kayan aiki masu inganci wajen gwajin cutar ta Covid-19 wanda a cewarta hakan ita ce guda daga cikin hanyoyi na gano masu dauke cutar cikin hanzari da kuma dakile bazuwarta.

Kasashen da za su ci moriyar wannan shiri sun hada da Najeriya da Masar da Kenya da Thailand. Sauran su ne Vietnam da Cuba da kuma Peru. Hukumar ta IAEA ta ce wadannan kasashe su ne na farko da za su ci moriyar wannan shiri, kuma a cewarta ta kashe kudin da suka kai dala miliyan hudu da rabi waje samar da kayan gwajin da kuma aikewa da su ga kasashen da ke bukata.