1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta sake nazarin dokar kulle

Abdul-raheem Hassan
November 16, 2020

Hukumomin Jamus za su duba yiwuwar ko za a cigaba da barin makarantun kasar a bude ko kuma za a rufe, tare da duba bukatar tsaurara matakan yaki da cutar Coronar.

https://p.dw.com/p/3lLOX
Bundeskanzlerin Merkel Coronavirus  Maske
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angele Merkel za ta sake ganawa da masu ruwa da tsaki na jihohin kasar 16 a wannan Litinin domin tattauna matsaya da tasirin kwarya-kwaryar dokar kullen da kasar ta sa a baya-bayannan.

Rahotanni na cewa an samu karuwar adadin masu kamuwa da cutar bayan sanya kwarya-kwaryar dokar kullen da ta shafi rufe gidajen abinci da barasa, yayin da gidajen tarihi da makaratu da wuraren ibada suka kasance a bude. Sai dai dubban 'yan kasar sun yi zanga-zangar adawa da dokar.