Jamus ta fara mayar da 'yan kasarta China
May 30, 2020Kamfanin jirgin sama na kasar Jamus Lufthansa ne ya fara wannan jigilar, wace ta kunshi Jamusawa da ke a aiki a matsayin manyan jami'ai a kamfanonin kasa da kasa da ke kasar ta China. Wannan dai shi ne karon farko da wata kasa a nahiyar Turai ke sake mayar da 'yan kasarta China tun bayan da aka kwashe su a lokacin da corona ta bunkasa a Chinar.
Hukumar bunkasa kasuwanci ta Jamus ce ta jagoranci wannan jigila, inda Jens Hildebrandt, babban darektan hukumar ke cewa, fara komawar Jamusawa kasar China wani babban ci gaba ne a kokarin da kasashen biyu ke yi na farfado da tattalin arzikinsu bayan da coronavirus ta dakatar da harkokin kasuwanci a tsakaninsu.
Jamus dai na da kamfanoni sama da 5,200 da ke aiki a China, inda suke samar da ayyuka fiye da milyan daya a kasar.