Corona: Kasuwanci tsakanin Jamus da Afirka ya samu nakasu
September 29, 2020Lokaci ya canza, yayin da a shekarun baya-bayan nan kamfanonin Jamus suka yi ta murna cewa huldar cinikaiya tsakanin Jamus da Afirka za ta habaka fiye da kima, amma murnarsu ta koma ciki a bana. Daga watan Janeru zuwa Juli kayayyakin da Jamus ta sayo daga Afirka sun ragu zuwa na Euro miliyan dubu 10.4 wato sun ragu da Euro miliyan dubu 3.6 idan aka kwatanta da na 2019, haka nan kayayyakin da Jamus din ta sayar wa Afirka nan ma an samu koma-baya, a jamilce dai ragin ya kai tsakanin kashi 18 zuwa 26 cikin 100 kamar yadda Heiko Schwiderowski shugaban sashen kula da ciniki da kasashen Afirka Kudu da Sahara a Cibiyar Ciniki da Masana'antu ta Jamus ya yi bayani.
"Kamar a sauran sassan duniya, huldar ciniki da Afirka ta samu nakasu. A bana muna hasashen cewa kayayyakin da Jamus za ta sayar a Afirka zai samu koma-baya da kashi 25 cikin 100. Hakan na kuma ba ma jin za a kara yawan jarin da ake zubawa a bana."
Kimamin kashi 82 cikin 100 na kamfanonin Jamus da ke a Afirka da kuma a yankin Gabas ta Tsakiya na fargabar samun koma-baya a kudaden shiga. Rabinsu ma na shirin rage yawan ma'aiktansu a kasashen Afirka ta Kudu da Najeriya, da ke zama mafiya karfin tattalin arziki a Afirka. Bayanan da babban bankin Jamus ya bayar na nuna cewa jari kai tsaye da kamfanonin Jamus suka saka a Afirka a watanni shidan farko na wannan shekara ya tsaya kan Euro miiyan 605, wato ya ragu da Euro miliyan 144 idan aka kwatanta da 2019. Wannan babban koma-baya ne ga nahiyar, wadda a kowace shekara ke da matasa kimanin miliyan 20 da ke nema sabbin guraben aikin yi. James Shikwati masani ne kan ayyukan raya kasa da ke birnin Nairobi na kasar Kenya ya ce harkoki sun tsaya cak.
"Wannan na nufin an tsaya waje guda. Kuma hasashen da aka yi na samun bunkasar tattalin arziki a kasashen Afirka Kudu da Sahara, ba zai tabbata ba. Abubuwa ba sa tafiya, ba a kirkiro sabbin aikin yi."
Halin da ake ciki na zama abin damuwa ba ga gwamnatocin Afirka kadai ba, hatta a nan Jamus ma shugabanni na nuna damuwa. Tun a wasu shekaru suke matsawa kamfanonin Jamus da su kara yawan jari da suke sakawa a Afirka ba kawai don gogayya da China ba, a'a don yaki da yunwa da talauci da kuma watakila yawan masu ci-rani daga Afirka zuwa Turai.
Sai dai masani kan ayyukan raya kasa a Kenya, James Shikwati ya ce har yanzu ba a rasa damar yin haka ba.
"Har yanzu Afirka na ba da dama ga kamfanoni da ke da sha'awar zuba jari a nahiyar don su kara kaimi na fara wasu sabbin aikace-aikace. Afirka babban zaure ne da haka zai iya faruwa."
Yanzu haka dai wasu kasashen Afirka sun fara sassauta tsauraran matakan yaki da corona da suka dauka, an fara bude kan iyakoki da filayen jiragen sama tsakanin kasa da kasa da nufin farfado da harkokin tattalin arziki da zirga-zirgar jama'a.