1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar corona na ci gaba da kamari a duniya

Abdoulaye Mamane Amadou
July 26, 2020

Fiye da mutana miliyan 16 sun kamu da annobar corona a duniya, a yayin da wasu kusan dubu 700 cutar ta yi sanadiyar rasuwarsu kamar yadda wasu alkaluman bincike suka bayyana.

https://p.dw.com/p/3fw0W
Spanien Coronavirus Menschen mit Masken
Hoto: picture-alliance/Zumapress/J. Merida

Har yanzu Amirka ce ke kan gaba na adadin wadanda suka fi mutuwa da mutum sama da dubu 146, yayin da Barzil ke biye mata da mutane sama da dubu 86 da suka rasu sai Birtaniya da mutane kusan dubu 46.

Nahiyar Afirka na daya daga cikin wasu yankunan duniya da cutar ta shafa inda daukacin kasashen nahiyar ke da adadin mutane dubu 17 da 513 da suka rasu.

Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa kasashe da dama na ba sa aiwatar da gwajin kamar yadda ya kamata, a yayin da wasunsu ke yin gwajin kawai ga wadanda rashin lafiyarsu ta tsananta.