Corona ta kashe mutane 2000 a Brazil
March 12, 2021Ma'aikatar lafiya ta Brazil ta ce annobar corona ta halaka fiye da mutun 2000 a kasa da sa'o'i 24 da suka gabata. Wannan ita ce rana ta biyu a jere da kasar da ke yankin Latin Amirka ke samun adadin mai yawa na wadanda annobar ta yi sanadiyar mutuwarsu.
Ko baya ga wadanda suka mutun ma, hukumomi a wannan kasa sun tabbatar da samun mutane dubu 75 da suka kamu da cutar, lamarin da ya kara ta'azzara al'amura.
Tuni ma dai majalisar dokokin kasar ta Brazil ta yi sauyi ga kundin tsarin mulki da gagarumin rinjaye, domin samun damar tallafa wa jama'a da kudi kusan Euro biliyan 6.8, don sake farfado da harkokin tattalin arzikin kasar, Sai dai har yanzu a na dakon shugaban kasar Jair Bolsonaro ya rattaba wa gyaran kundin tsarin mulkin hannu don ya fara aiki.