1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalibai sun kamu da Corona a Indonesiya

September 2, 2020

Dalibai sama da 600 a wata makarantar kwana ta kasar Indonesiya sun kamu da Corona inda kuma aka killace wasu domin hana yadata ga sauran jama'a.

https://p.dw.com/p/3huNq
Indonesien Jakarta | Covid-19 Task Force Sprecher - Wiku Adisasmito während Online Konferenz
Hoto: Humas BNPB

An dakatar da zuwa makaratu ga dalibai a yankin Banyuwangi na kasar Indonesiya, bayan da aka samu dalibai 664 dauke da Corona tare da killace wasu 6000 a wata makarantar kwana. un dai a tsakiyar watan Ogusta ne aka fara gwajin Corona ga daliban, yayin da suka fara korafe-korefe rashin lafiyar da ke nuna alamun Corona. Mai magana da yawun ministan lafiyar kasar Benget Saragih ya ce an dakatar da duk wata mu'amulla a tsakanin daliban kuma tuni jami'an tsro suka killace wurin da makarantar take.

Hukumomin lafiyar kasar ta Indonesiaya sun ce an samu karin mutane sama da 3000 dauke da cuta,r wanda ya kai yawan masu fama da Corona a kasar suka zarce 180,000. Tuni kuma sama da 7,616 suka ce ga garinku nan.