1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu za ta je kotu a kan dokar corona

June 5, 2020

Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ce za ta daukaka kara a kan yadda wata kotu a kasar ta ayyana cewa wasu matakan kariya da take dauka na coronavirus sun sabawa doka.

https://p.dw.com/p/3dHEX
Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: AFP/M. Spatari

Wani babban jami'in gwamnatin kasar ya sanar da haka a wannan Alhamis jim kadan bayan taron ministocin kasar. A watan Maris din da ya gabata kasar ta sanya dokoki wanda ake ganin sun yi tsauri wurin takaita bazuwar coronavirus. Dokokin da jama'ar kasar ke ta guna-guna akai sune hana shan barasa da hana sayar da taba sigari da mahukumta suka yi da sunan coronavirus, inda wata kotun kasar ta ce irin wadannan dokoki sun sabawa doka. Sai dai da alama gwamnatin Cyril Ramaphosa ba ta ji dadin wannan hukunci ba, kuma ta ce za ta daukaka kara.