1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta ragewa bikin Good Friday armashi

April 2, 2021

An samu karancin masu ziyara a wuraren ibadu a wannan lokaci na bikin Good Friday sakamakon Corona.

https://p.dw.com/p/3rWwW
Heiligen Grab in Eichstätt
Hoto: Eikelmann

Kiristoci a fadin duniya na gudanar da bikin Good Friday a cikin yanayi na annobar corona, wannan shi ne karo na biyu da ake bikin cikin wannan yanayin, inda aka samu karancin masu zuwa ibada a birni mai tsarki na Jerusalam ko kuma Birnin Kudus.

Sai dai an gano wasu masu ibada na wake-waken yabo a kusa da cochin Sepulchre da aka yi ammana nan ne aka gicciye Annabi Isah AS.

A can Vatikan kuma, Shugaban Darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya kai ziyara wani gidan gajiyayyu albarkacin wannan rana, haka zalika Paparoma Benedict mai murabus shi ma ya albarkaci wannan rana ta hanyar yin kira ga al'umma da su amince da rigakafin corona.