Corona ta yi wa duniya dabaibayi
Kimanin shekara guda da ta gabata ce annobar corona ta bulla a sassan duniya daban-daban. Fiye da mutane 100 ne suka kamu da cutar, yayin da a share guda cutar ta yi sauyi kan yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu.
Ba da tazara
Wadannan mutanen a Singapore na kallon fim ne a wani budadden waje inda suka ba da tazara, sai dai hakan ba abu ne da wasu kasashe za su iya yi ba a halin yanzu. Hukumomi a kasar sun alakanta karancin masu dauke da cutar ta yadda ake sanya idanu kan mutane tare da taimakon wata manhanja.
Halin kunci a Afirka ta Kudu
Afirka ta Kudu na kan gaba wajen yawan masu corona a Afirka, inda fiye da mutane miliyan guda suka kamu. Kasar na daga cikin wadanda suka samu bullar wani sabon nau'in cutar wadda ke saurin yaduwa tsakanin al'umma.
Daukar matakan kariya a wuraren shakatawa
Al'umma a Ostireliya kan fita wuraren shakatawa musamman ma bakin ruwa, sai dai ana kokari wajen daukar matakan kariya don gudun yaduwar cutar. An sanya alluna din tunatar da jama'a muhimmancin ba da tazara.
Takaici na rasa dan uwa
Nan wata budurwa ce 'yar shekaru 14 mai suna Kelvia Goncalves take kuka na rashin mahaifiyarta Andrea dos Reis Brasao a garin Manaus, Brazil. Brasao ta rasu ne tana da shekaru 39 kacal. Matar na daga cikin mutane da dama da corona ta hallaka. 'Yan kasar da dama dai sun zargi shugaban kasar da gaza yin abin da ya kamata wajen dakile yaduwar cutar.
Gudanar da gwaji tsakanin jama'a
Jami'an kiwon lafiya a Hong Kong kan bi lunguna da sukunan kasar wajen yin gwaji na cutar corona. A lokuta da dama an sanya dokar kulle a yankunan da cutar ta yi kamari kuma yankin na Hong Kong kan yi koyi da matakan yaki da cutar da China ke amfani da su.
Amfani da sabbin hanyoyi na cudanya da jama'a
Zuwan corona ya sanya gudanar da taruka ta shafukan intanet, sai dai makadan nan na Flaming Lips sun zo da wani sabon salo don nishadantar da masoyansu. A birnin Oklahoma da ke Amirka, makadan sun shirya wani wasa inda kowa ya kasance cikin wata balan-balan. Hakan ya sanya jama'a halartar wasan da suka yi ba tare da fargabar harbuwa da corona ba.
Gudanar da rigakafi a wuraren ibada
Sakamakon rufe wuraren ibada musamman ma majami'u a Birtaniya, hukumomi sun yi amfani da irin wadannan wuraren don gudanar da rigakafin corona kamar yadda ake gani a wannan majami'ar da ke Lichfield a birnin Birmingham.
Fatan samun nasara a yakin da ake da corona
Wannan matar 'yar Masar mai suna Amy Ezzat ta shirya cake da ke da zubi irin na allurar rigakafin corona inda aka rubuta ''Rigakafin Corona'' da kuma ''Bankwana da Corona''. Amy ta rabar da cake din ne ga marasa lafiya da ke fama da corona a Alkahira. Duk da cewar har yanzu wasu jama'a ba su samu damar karbar rigakafin corona ba, da dama na ganin ita ce kadai mafita a yakin da ake da annobar.